Jajirtaccen soja ya rasu a fadar shugaban kasa ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998.

Tunawa da mahaifin ta, babbar diyar sa Gumsu Sani Abacha bata boye cewa suna kewar shi. Tayi masa addu'a Allah ya jikan shi rahama.

Ta wallafa hoton sa mai dauke da shekarun da ya rasu tare da rubuta "shekaru 20 kenan, Allah ya tsarkaka ruhin ka. Allah ya yafe maka kura-kuran ka, Ya sa Aljannah ce makomar ka" a shafin ta na Instagram.

"ALLAH ya jikan ka da rahamar sa. We miss you so much"ta kara.

[No available link text]

Ba tare da yin wani kari, ga wasu abubuwa da ya kamata mu sabi game da tsohon shugaban wanda yayi mulki na tsawon shekaru biyar kamar haka:

 • Asali shi dan kabilar Kanuri ne dake jihar Borno sai dai an haife shi a jihar Kano kuma nan ya girma wanda daga baya ya mayar a matsayin mahaifar shi
 • ya shiga aikin soja a shekarar 1963 da matsayin 2nd Liutenan bayyan kammala karatu a makarantar soja na Mons Defence Officers Cadet Training College dake kasar Ingila.
 • Ana tunanin cewa yana tare da sojoji da suka yi juyin mulki a 1966 wanda tayi sanadiyar mutuwar shugaban kasa na lokacin Manjo-janar Johnson Aguiyi-Ironsi.
 • Bayan juyin mulkin da ya faru a shekarar 1988 wanda yayi sanadiyar tsige Buhari, Abacha ya sanar da janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin sabon shugaban kasa ga bainar jama'a.
 • Kasancewa shine sakateren ayyukan tsaro a zamanin, ya hau karagar mulki a cikin shekarar 1993 bayan shugaba mai rikon kwarya na lokacin yayi murabus.
 • Karkashin mulkin sa nijeriya ta mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arzikin man fetur.
 • Magoya bayan sa da masana a kan harkokin kasuwanci sun yaba masa bisa tsarin da ya gudanar a harkar kasuwanci da tattalin arzikin kasa duba da yadda ya jajirce wajen daga darajar naira.
 • Ya taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro da dimokradiyar a kasashen Saliyo da Liberiya bayan kasashen sun kwasi shekaru da dama ana yaki a kasashen.
 • Auren shi da matar shi
 • Shine soja daya tilo a tarihin soja na kasar da aka daga matsayin sa daya bayan daya ba tare da samun cikas har matsayin Janar mai cikakken tauraro.
 • Karkashin mulkin sa aka kafa asusun PTF wanda shugaban kasa na yanzu ya jagoranta. Asusun ta tallafa wajen gina wasu muhimman ayyukan cigaba na kasa.
 • Ya rasu a fadar shugaban kasa a cikin shekara 1998. Sai dai ana cece kuce game da asalin abun da yayi sanadiyar mutuwar sa amma hakikanin sanarwa da aka fitar ma jama'a shine cewa ya rasu sakamakon bugun zuciya da ya samu.

Tsohon shugaban ya sha yabo da soka game da yadda ya gudanar da lamuran kasar yayin da ya kai kan karagar shugabanci.

Ana ganin mulkinsa na cike da cin zarafin bil'adam da take 'yancin fadin albarkacin baki.

A kwannan baya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuna dashi inda ya bayyana da cewa yayi kokari matuka wajen gyara tituna a kasar.

Shugaba Buhari wanda yayi aiki a matsayin shugaban asusun PTF a zamanin mulkin Abacha yana mai cewa "Ba tare da yin la'akari da ra'ayi da kuke dashi game da Abacha, na amince da yin aiki tare dashi kuma tituna da muka gina tare da wasu muhimman ayyukan da muka kaddamar da asusun PTF sun birge" ya bayyana yayin da yake zantawa da masu yakin neman zaben sa.