Pulse.ng logo
Go

Daurin shekara 14 "A sassauta mun, gidan yari akwai cinkoso" tsohon gwamna ya roki kotu gabanin hukuncin dauri da aka zartar masa

Gabanin samun hukuncin, alkalin shi Paul Eroko ya roki kotu da ta sassauta hukunci kan laifin shi kasancewa wasu bata gari suka zuga shi wajen aikata laifin.

  • Published:
Have mercy, prisons are congested, Dariye begs court play Kotu ta daure tsohon gwamnan jihar filato (Guardian )

Tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye ya nemi rangwame yayin da aka zaman sauraron karar laifin wawure kudin jiha da EFCC ta shigar a kansa.

A zaman kotu da aka yi ranar talata 12 ga watan Yuni mai sharia Adebukola Banjoko ta yanke masa hukuncin dauri na shekara 14 bayan kama shi da laifin wawure kudin jama'a.

An kama shi da laifin wawure naira biliyan daya na daga cikin asusun muhalli da halittu sanda yake gwamna.

Gabanin samun hukuncin, alkalin shi Paul Eroko ya roki kotu da ta sassauta hukunci kan laifin shi kasancewa wasu bata gari suka zuga shi wajen aikata laifin.

Wakilin tsohon gwmnan ya roki mai sharia da ta yi ma Dariye afuwa tare da sanar cewa akwai cinkoso a gidajen yari.

Sai dai wakilin EFCC, Rotimi Jacobs ya mayar masa da martani inda ya jaddada ma kotu cewa hukuncin yayi masa daidai bisa ga laifin da ya aikata.

Ganin martanin da wakilin EFCC ya bada, Joshua dariye ya nemi a bashi damar yin magana.

"A sassauta mun, gashi kai kirista ne kuma sunan ka jacob" Ya roki wakilin EFCC.

Sai dai rangwamin da ya nema bata yi tasiri ba inda daga bisani mai shari'a ta zartar da hukunci.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.