Wata babbar kotu dake gudanar da zamanta a garin Oshogbo a jihar Osun ta amince da sauraran bukatar da wasu alkalai suka shigar na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babban mai shari'a a kotun, Justice Onyetenu, ta amince da bukatar da wasu lauyoyi dake rajjin kare hakkin dan Adam suka shigar.

Cikin bukatun da suka shigar game da lamarin, akwai batun takardar shaidar kammala karatun sekandare na shugaba. Kamar yadda suka bayyana ma kotun, wadanda suka shigar da karar sun zargi shugaban da sabawa kundin tsarin kasa bayan rantsar dashi da takarda da suka kira na bogi.

Sauran bayanai da suka gabatar gaban kotun da suke kalubalantar Buhari sun hada da gazawar gwamnati wajen kawo karshen yawaitar kashe-kashe da rikicin makiyaya da manoma.

A rahoton da BBC ta fitar, daya daga cikin alkalan da ya shigar da karar, Kanmi Ajibola, ya bayyana cewa kotu ta amince da bukatar da suka shigar bayan ta gamsu da hujjojin da suka shigar.

Kotun dai ta dage sauraron wannan karar zuwa 30 ga watan Oktoba 2018.