Pulse.ng logo
Go

Aikin arziki Tauraruwar Kannywood ta raba kayan masarufi ga mara hali

Jarumar wanda aka fi sani da Hadiza Gabon tayi hakan ne a garin Kano kuma aiki ne wanda ta saba yi a ko wace shekara.

  • Published:

Tauraruwar fina-finan hausa ta masana'antar Kannywood, Hadiza Aliyu ta tallafa ma wasu mara hali kayan masarufi don raya watan mai alfarma.

Jarumar wanda aka fi sani da Hadiza Gabon tayi hakan ne a garin Kano kuma aiki ne wanda ta saba yi a ko wace shekara.

Bisa wannan kokari da tayi, jarumi wanda aka yi ma lakabi da Sarkin kannywood, Ali Nuhu ya yaba mata tare da wallafa hoton ta sanda take gudanar da rabon kayan masarufin a shafin sa na Instagram.

Hadiza Gabon ta raba kayan masarufi ga mabukata play

Hadiza Gabon ta raba kayan masarufi ga mabukata

(Instagram/realalinuhu)

 

Tun ba yau ba, jarumar tana daya daga cikin fitattun masana'antar fim dake tallafawa mara sa galihu da arzikin da Allah ya azurta ta dashi.

Tana hakan ne a karkashin gidauniyar ta mai suna Hadiza Aliyu Gabon Foundation.

Hazikar jarumar tana daya daga cikin manyan jarumai da ake damawa dasu a masana'antar fim bisa rawar da take takawa a fim ta hanyar nuna kwarewar ta a ko wani matsayi da aka bata.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.