Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya watau NFF ta tabbatar da cewa wasan tawagar super eagles na gaba zaa ta buga ne a filin wasan Ahmadu Bello dake nan garin Kaduna.

Wannan shine karo na farko da tawagar zata yi amfani da filin bayan wasan ta ta da tawagar kasar Masar a cikin shekarar 2016.

Zaben filin ya biyo bayan binciken da kocin tawagar yan wasan Gernoht Rohr yayi.

NFF tace ta sanar ma hukumar kwallo ta Afrika game da wajen da za'a buga wasan kuma bisa ga binciken da kocin Nijeriya yayi a filin duk wata gyara da ya kamata a yi za'ayi shi gabanin wasan.

Tawagar yan wasan zasu kece raini da na kasar Libya cikin jerin wasanin neman shiga gasar kofin Afrika da za'a buga shekara mai zuwa.

Nijeriya zata buga wasan ta na uku na rukunin D da da kasar arewacin afrika ranar 10 ga watan Oktoba.

Wasan ta na farko Nijeriya ta fadi inda kasar Afrika ta kudu ta doke ta da ci biyu babu. Wasan ta na Biyu Nijeriya ta lallasa kasar Seychelles da ci uku babu ko daya.

Tawagar zasu nemi su tabbatar da matsayin su domin shiga gasar afrika da anniyar samun galaba akan Libya.

A halin yanzu Nijeriya ce na uku a rukunin D da maki uku yayin da Libya da Afrika ta kudu suka raba maki hudu hudu kuma suka zama na jagororin rukunin.