ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kaddamar da sabuwar rigar tawagar Super eagles na gasar cin kofin duniya (Hotuna)

Yan wasa Mikel Obi da Alex Iwobi tare da Wilfred Ndidi da Kelechi Iheanacho da mawaki Wizkid sun halarci bikin kaddamar da sabuwar rigar tawagar Nijeriya na buga gasar world cup

Rigar tayi shigen irin wanda tawagar super eagles suka sanya a gasar FIFA world cup na shekarar 1994.

An gudanar da bikin kaddamarwa a birnin London ranar laraba 7 ga watan yau.

Jagoran yan wasan tawagar Super eagles Mikel Obi tare da Alex Iwobi da Kelechi Iheanacho da Wilfred Ndidi sun halarci bikin.

Shima shahararen mawakin Nijeriya Wizkid ba'a baro shi baya ba wajen halartar wannan bikin na fitar da rigar sanyawa na kasar tashi.

ADVERTISEMENT

A cikin faifon bidiyo da kamfanin Nike ya fitar, yan wasan sun nuna farin cikin su bisa yadda aka kira rigar shige irin ta adon zamani.

Suma yan Nijeriya sun tofa albarkacin bakin su kafafen sada zumunta game da wannan rigar wanda tayi fice daga jerin rigar sanyawa da tawagar ta taba sanyawa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT