ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sojoji sun kama wani gawurtaccen dillalin bindigogi a Kaduna

An kama mai safarar makamai ga a garin Rigachukun dake nan kaduna ranar litinin 19 ga wata

Kakakin rundunar sojoji na kasa  ya bayyana kamun a wata takarda da ya fitar ga manema labarai ranar litinin 19 ga wata.

Ya kara da cewa an kama bindigogi kirar AK-47 guda biyu da harsashin bindiga daga hannun dillalin mai safarar makamai ga yan fashi.

Kakakin ya kuma bayyana cewa sakamakon yawon hare-hare na fashi da makami da al'ummar rigachukn ke fuskanta ana tura dakarun yankin domin dakile tarzomar da al'ummar ke fuskanta.

Daga karshe ya sanar cewa sojojin kasa sun tsara matakai na a kare jama'a daga hare-haren miyagun yan fashi da makami da barayin shanu da masu garkuwa da mutane.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT