Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya daura aniyyar tsayawa takarar dan majalisar dattijai na Kano ta tsakiya, kujerar da a yanzu tsohon gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso yake kai.

Ya ce ya koma APC ba tare da gindaya wasu ka'idoji na cewa ga abin da yake so ba.

A labarin da BBC ta fitar tsohon gwamnan kano yace tun daga lokacin da ya yanke shawarar fita daga PDP ya ajiye anniyarsa na yin takarar shugaban kasa.

Shekarau wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2015 yace ba zai soma batun neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba a 2019, domin tuni jam'iyyar ta yanke hukuncin cewa Shugaba Buhari ne dan takarar ta.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa ba ya jin tsoron kara wa da ko waye daga jam'iyyar APC, ko da kuwa Kwankwaso ne zai sake yin takarar.

Ya ce ko da Kwankwason ne zai sake yin takarar, babu wani abin fargaba, domin a shirye ya ke ya kara da ko ma wanene.