Pulse.ng logo
Go

Zauren majalisar dokoki Saraki ya rantsar da sabbin sanatoci

Ahmed Babba-Kaita da Lawal Gumau sunyi nasarar lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Bauchi da Katsina cikin watan Agusta.

  • Published:
The minister of information and culture, Lai Mohammed has said that the exit of Senate President Bukola Saraki from the All Progressives Congress (APC) will not affect the party. play

Senate President Bukola Saraki

(NASS)

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya rantsar da sabbin Sanatoci Ahmed Baba-Kaita da Lawal Gumau shigar su farfajiyar majalisar.

An rantsar dasu a zaman da majalisar tayi ranar 10 ga watan Oktoba.

Sanatocin sunyi nasarar lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Bauchi da Katsina.

Ahmed Babba-Kaita yayi nasarar lashe zaben cike gurbin da aka gudanar a watan Agusta na wakiltar arewacin jihar Katsina karkashin jam'iya mai mulki ta APC.

Ya doke dan uwan shi na jam'iyar PDP a zaben domin maye gurbin marigayi Bukar Mustapha a majalisar dokokin tarayya.

Shima Lawal Gumau yayi nasarar lashe zaben jihar Bauchi wanda aka gudanar ranar 11 ga watan Agusta karkashin jam'iyar APC.

Zai wakilci yankin kudancin jihar Bauchi a zauren majalisar dattawa bayan yayi nasarar maye gurbin marigayi Ali Wakili wanda ya rasu cikin watan Maris na 2019.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement