Pulse.ng logo
Go

Ziyara zuwa kasar Ingila Shugaba Buhari ya gana da firayi minista Theresa May

Shugaban yayi ma kasar godiya bisa goyon da take bayarwa ga sojojin Nijeriya wajen yakar ta'adanci

  • Published:
Theresa May tells Buhari to invest in young people for prosperous future play

British Prime Minister, Theresa May with Nigeria's President Muhammadu Buhari

(Twitter/@BashirAhmaad)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara ma firayi ministan Ingila Theresa May a fadar gwamnatin kasar dake Downing street nan birnin Landan.

Ana zaton jagororin sun tattauna kan dangantaka dake tsakanin kasar Nijeriya da Ingila.

Mai yi shugaban kasa hidima kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad, ya wallafa cewa bayan tattaunawan su, shugaba Buhari yayi ma birtaniya godiya bisa matakin horon sojojin Nijeriya wajen yaki da ta'adanci.

 

Ziyara zuwa kasar Ingila

Tun ranar 9 ga wata Afrilu shugaba Buhari ya kai ziyara kasar Ingila. shugaban ya gana da amin shi babban limamin cocin Centerbury, Justin Welby. Hakazalika shuban zai kuma ziyarci taron kasashe rainon birtaniya.

Bayan haka Shugaban zai kuma tattauna da shugaban kamfanin Dutch royal plc mista Ben van Beurden da kamfanin Shell da makamantan su kan matakin zuba jari a masana'antar mai na kasar Nijeriya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.