ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaban ƙasa ya sauka garin Abuja

Shugaban ya koma Abuja yayin da mataimakin shi ya tafi jihar Benue don jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja ranar laraba 6 ga watan Satumba bayan hutun sati daya ya yi a daura na bikin babban sallah.

Shugaban ya sauka birnin tarayya tare da uwargidan sa Aisha Buhari, kakakin sa Garba Shehu, babban jami’i na tsaro Bashir Bindawa da sauran fadawan shi.

Buhari ya koma mahaifar sa Daura ranar laraba 30 ga watan Agusta inda ya kaddamar da bikin babban sallah.

Shugaban ƙasa ya soke zaman majalisar ministoci da ya kamata ayi yau kasancewa ministan labarai Lai Muhammed yace bai samu lokaci na shirya takardun da zasu tattauna akai.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya koma Abuja yayin da mataimakin shi ya tafi jihar Benue don jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa.

Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya gana da gwamnan jihar Samuel Ortom tare da manyan ma’aikatan gwamnati na jihar inda ya tabbatar masu cewa gwamnatin tarraya zata cigaba da taimaka ma jihar.

Osinbajo ya ziyarci kasuwar Benue inda aka sanya wadanda ambaliyyar ya raba da muhallinsu.

A kiyasin da hukumar agaji na gaggawa na jihar tayi akalla mutane 110,000 cikin shiyoyi 24 dake garin Makurdi ne ambaliyyar ya shafa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT