Pulse.ng logo
Go

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Shekara 11 da rabuwa da fiyayen malamin addini

Ya rasu ranar juma'a kimanin  karfe 5:30 na safe yayin da yake jagorantar sallar asuba a babbar massallacin juma'a dake unguwar Dorayi nan Kano

  • Published:
Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya cika shekara 11 da mutuwa play

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya cika shekara 11 da mutuwa

Safiyar ranar 13 ga watan Afrilu na 2007 shekara sha daya baya, kasar Nijeriya da ma kasashen musulmai sun girgiza, mutuwar daya daga cikin jagororin addinin musulunci kuma kundin ilimi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam.

Ya rasu ranar juma'a kimanin  karfe 5:30 na safe yayin da yake jagorantar sallar asuba a babbar massallacin juma'a dake unguwar Dorayi nan Kano.

Abun bakin ciki shine ganin yadda wasu yan bindiga suka shiga masallaci har suka bindige shi. An harbe shi a kirjin sa da kuma wurin cibiyar shi.

An gaggauta kaishi asibiti domin ceto rayuwar shi sai Allah ya riga ya rabuta ajalin sa.

Malamin ya kasance jagora duba da irin rawar da ya taka tare da gudumawar da ya bada wajen raya addinin musulunci da kuma daura al'umma tafarkin turbar fiyeyen halitta.

Takaitaccen tarihin Sheikh Ja'afar

ga takaitaccen tarihin marigayi Sheikh ja'afar Mahmud Adam kamar yadda jaridar Rariya ta fitar.

An haifi marigayi Sheik Jafar a garin Daura ranar 12, ga watan Febrairu, 1960, ya rasu ranar 13, ga watan Afrilu 2007. Ya fara karatu a makarantar horar da malamai ta Gwale, cikin shekarar 1984. Ya kuma kammala karatunsa cikin shekarar 1988.

Cikin shekarar 1989 ya samu shiga jami'ar addinin musulunci, wacce take gari Madina. A nan ma ya yi shekaru hudu yana karatu, ya kammala shi cikin shekarar 1993.

Yana dawowa gida bai yi wata-wata ba ya kama wa'azi, ya kuma kafa cibiya mai suna Usman Bin Affan. Cikin shekarar 1995, wannan cibiyar ta shahara kuma ta zama wacce take cin gashin kanta. Yana koyar da mutane da yawa karatu na addini, duk watan Azzumin Ramadan, ya kan yi tafsiri a garin Maiduguri.

Ya yi digiransa na uku, wato digirin digirgir, a jami'o'in Bayero da Danfodio. Sannan zuwansa Kano daga Daura, ya yi karatu irin na Alo, sannan, ya yi dalifta, a wurin maluma da yawa a Kano.

Har ila yau shi ne shugaban asusun wannan cibiya ta Usman Bin Affan. Ya wakilci Nijeriya a gasusukan karatun Al'kur'ani a lokuta daban-daban. Yana cikin kwamitin Malamai na jihar Zamfara da Bauchi. Yana gudanar da karatuttuka a gidajen rediyo, da talabijin daban-daban. Kamar Rediyo Kaduna, Bauchi, ARTV Kano, DITV Kaduna NTA Borno, OITV Damaturu da NTA a Yola.

Allah ya jikan shi da Rahama, Ameen.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.