Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Usman Babatuni Zaria ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Marigayin shine limamin masallacin NNPC na Kaduna kuma ya rasu a asibitin koyo ta jami'ar Ahmadu Bello dake Shika inda yake jinyar ciwon suga.

Tuni aka yi jana'izatr sa a garin Zaria kana a binne shi a makabartar Dambo dake nan Zazzau.

Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kana ya bara mata biyu da yara 21.