Pulse.ng logo
Go

Sheikh Usman Babatuni Zaria Shahararren malamin addini ya rasu

Tsohon shugaban kungiyar limamai na jihar Kaduna ya rasu a yammacin ranar litinin 10 ga watan Satumba.

  • Published:
Sheikh Usman Babatuni ya rasu yana da shekaru 75 a duniya play

Sheikh Usman Babatuni ya rasu yana da shekaru 75 a duniya

(JIBWIS)

Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Usman Babatuni Zaria ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Marigayin shine limamin masallacin NNPC na Kaduna kuma ya rasu a asibitin koyo ta jami'ar Ahmadu Bello dake Shika inda yake jinyar ciwon suga.

Tsohon shugaban kungiyar limamai na jihar Kaduna ya rasu a yammacin ranar litinin 10 ga watan Satumba.

Tuni aka yi jana'izatr sa a garin Zaria kana a binne shi a makabartar Dambo dake nan Zazzau.

Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kana ya bara mata biyu da yara 21.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement