ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Buhari ya kare kanshi daga gubar El-rufai - inji sanata

Tun ba yau ba sanatan da gwamnan ke gamawa a kan harkar siyasa

Sanata Shehu Sani yayi ma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari gargadi na ya kiyaye halakar shi da gwamnan jihar kaduna Malam Nasir El-rufai.

A wani rahoto da jaridar punch ta fitar dan majalisa mai wakiltar yankin jihar Kaduna ta tsakiya ya kira gwamnan da siffar maciji mai dauke da guba wadda ke neman bata aminci dake cikin jam’iyar APC na jihar shi har ma da ƙasar baki daya.

Dan majalisar yayi wannan furucin bayan amincewar da jam’iyar APC na jihar kaduna tayi wa gwamnan.

Yace gwamnan yana nuna amince ga shugaban kasa don amfanin kansa kuma shugaba Buhari yayi watsi da ayyukan da gwamnan keyi na neman zaben 2019.

ADVERTISEMENT

Sanata yayi la’akari da cewa kada shugaban ya amince da gwamnan domin yayi ma tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'adua barazanar cewa zai kashe shi.

Tun ba yau ba sanatan da gwamnan ke gamawa akan harkan siyasa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT