ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wasu yan aikin ƙwadugo sun shiga hannun hukuma yayin da suke fashi da bindigar bogi

jami’in da ya gurfanar dasu yace yan banga suka kama su

An gurfanar da wani Ahmed Ogunjimi da Rashidi Abiola gaban kotu bisa ga zargi yin fashi a gidajen mutane da bindigar bogi.

Ogunjimi mai shekaru 30 asali mai aikin gini ne shi kuma Abiola mai gyaran mota ne. An gurfanar da su a bababn kotun majistere dake Ikeja babban birnin jihar Legas.

Masu laifin sun roki kotu da yin sassauta hukunci amma Mr J.A Adigun na kotun majistere ya basu damar yin beli a kan naira dubu dari (N100,000).

A bisa bayanin jami’in da ya gurfanare da su gaban kotu sgt. Godwin Awase, wadanda ake zargi sun aikata laifin ranar 1 na watan Satumba a dai dai karfe 2:00 na safe a nan titin Kudirat Abiola dake Ikeja.

ADVERTISEMENT

Yace sun aikata laifin tare da taimakon wasu da suka tsere a gidajen Uchenna Oluigbo, Lawrence Oyinda da Yusuf Abubakar da bindigar bogi.

Awase yace yan banga  na unguwar suka lama su yayin da suke neman yin fashin.

Laifin da ake tuhumar su dashi ya sabawa dokar jihar Legas kuma suna iya yin shekaru 7 a gidan yari indai an tabbatar da laifin.

Kotu dai ta daga jin karar zuwa ranar 28 na watan Satumba

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT