ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

A kulle magu don ya raina hukuncin shari’a - inji tsohon gwamna zuwa ga kotu

A ranar 13 ga watan Yuli ne mai shari’a Yusuf Halilu ya ba da izini na a sake shi daga hannun huƙuma

Former Jigawa governor, Saminu Turaki

A ranar litinin aka bukaci wani kotu dake birnin tarayya da ta yi wa shugaban huƙumar yaki da cin hanci da rashawa horo bisa ga zargin raina hukunci da shari’a ta fitar don yaki ya saki tsohon gwamnan jihar Jigawa bayan kotu ta bashi damar yin beli

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan wanda ake zargi da yin al’mumdahana da kudin jam’a ranar 4 ga watan Yuli a wani taro a garin Abuja bisa ga izinin da  kotun tarayya dake garin Dutse ta bada na huƙumar ta aikata haka a shekara 2014.

Tsohon gwamnan ya bukaci kotu da ta bi mashi hakkin shi inda don huƙumar ta tsare shi fiye da ƙwana biyu wanda yin haka ya tsaba ma ƙundun tsarin mulki.

A kwanaki baya mai shari’a Yusuf Halilu a ranar 13 ga watan Yuli ya ba da izini na huƙumar ta saki shi daga bisa ga sharudan beli.

ADVERTISEMENT

Cikin sharuɗan da aka ba tsohon gwamna, an bukaci shi da ya kawo mutum biyu wadanda zasu tsaya mishi kuma wadanda an tabbatar da sana’ar su kuma su kasance mazaunin garin Abuja.

Kotu ta umurce shi da ya ƙaddamar da takardun tafiya kuma ya kasance yana zuwa ofishin huƙumar a ko wani sati biyu

Duk da haka EFCC a ranar 14 ga watan Yuli ta nemi kotu da ta dakatar da belin da aka bashi.

Huƙumar EFCC tace sharuɗan beli da kotu ta bada tayi sassauci sosai kuma ta riga ta daukaka kara zuwa kotun tarayya na Abuja a dai-dai lokacin da kotu ta bashi izinin yin beli.

A wata kara da misis Regina Okotie-Eboh ta fitar a madadin shi, Turaki ya roƙi kotu da ta kama Magu don ya sabawa doka.

ADVERTISEMENT

Ya kara roƙon kotu da ta taimaka wajen ganin cewa huƙumar ta sake shi.

Mai shari’a Halili ya dakatar da jin karar sai zuwa 20 ga watan Yuli.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT