ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Bidiyon shahararren dan kwalo sanda yake wanke bahayan masallaci

Lamarin ya faru sa'o'i kadan bayan dan kwallon ya taimaki kungiyar sa wajen doke abokan adawar su a wasan gasar firemiya da aka buga ranar asabar.

Masallacin mai suna Al-rahman dake nan titin Mulgrave a birnin Liverpool na kasar Ingila nan ne dan wasan yake gabatar da sallolin sa.

Wasan da Liverpool tayi da kungiyar Leicester wanda aka tashi 2-1, dan kasar Senegal ya zura kwallo daya a raga wanda ya taimaki kungiyar sa wajen samun galaba a kan abokan adawar su.

ADVERTISEMENT

An haifi Mane ne a cikin addinin musulunci, kuma ya girma a garin Bambali dake kudancin kasar Senegal inda mahaifinsa ne limamin masallacin garin, hakan ya sanya shi mutumi mai riko da addini.

Dan wasan mai shekaru 26 a duniya yana daya daga cikin fitattun yan wasan kwallon kafa dake alfahari da addinin su. Yakan yi sujududa don nuna godiya idan yayi nasarar zura kwallo a raga.

Dan kwallo yana daya daga cikin yan wasa da ake jin duriyar su a duniyar kwallon kafa ta duniya a halin yanzu.

Yayi nasara lashe gwarzon dan wasan watan Agusta ta gasar firemiya sakamakon rawar da ya taka ma Liverpool a watan.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT