Ya samu matsayin ne bayan rasuwar tsohon shugaban rundunar yan sandan kasaAlhaji Ibrahim Coomasie wanda ke rike da sarautar gabanin rasuwar shi.
Wannan labarin ya fito ne a cikin wata sako da sakataren masarautar kuma mai sarautar 'Sallamar Katsina"Alhaji Bello Ifo ya sanar ma manema labarai.
Tsohon dan majalisar ya wakilci jihar Katsina a farfajiyar majalisar tarayya tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
Shine mai rike da sarautar 'Dan majen katsina' kafin wannan sabon sarautar da masarautar ta nada mashi.