Ya ce za a binne shi yau a Hubbaren Shehu, Sokoto, bayan Sallah na Zuhr. An ƙara bayani da cewa za a yi Sallah na Janaʼizar sa a Babban Masallaci Jumaʼa na Sarki Muhammadu Bello a wannan rana.
Marigayi Alhaji Ibrahim Dasuƙi shi ne Sarkin Muslumai daga 6 Nuwamba, 1988 zuwa 20 Afrilu 1996. An hambara shi daga kujera a lokacin Mulkin Soja na Marigayi Janar Sani Abacha. Kafin ya zama Sarki, an naɗe Alhaji Ibrahim da rawanin Baraden Sokoto. Dasuƙi shi ne Sarki na Farko daga Gidan Buhari, Jikan Usman Ibn Fodio. Da tasirinsa aka kafa Ƙungiyar Jamaʼatu Nasril Islam. An haife shi a ranar 31, Disamba 1923.
Allah (SWA) ya yi masa gafara. Allah ya yi masa rahama da Al-Jannah Firdaus. Amin