ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Rashin zuwa na Kano zalunci ne

Dan majalisar dattawa yana mai cewa wannan tsarin zalunci dake faruwa ba tsarin dimokradiya bane. Jagoran akidar kwankwasiyya yace irin wannan tsari tun a zamanin da aka yi watsi dashi domin an daina ire-iren mulkin kama-karya tun shekarun baya

Dan majalisar dattawa yana mai cewa wannan tsarin zalunci dake faruwa ba tsarin dimokradiya bane. Jagoran akidar kwankwasiyya yace irin wannan tsari tun a zamanin da aka yi watsi dashi domin an daina ire-iren mulkin kama-karya tun shekarun baya.

Hirar shi da wakilin BBC, kwankwaso soki rundunar yan sanda da taimakawa wajen haifar da tashin hankali. madugun ya bayyana cewa za'ayi garambuwal ga tsarin yan sanda nan gaba bisa ga ayyukan da suke aikatawa na rashin tsari.

A cewar shi "Da yawa zaka gan sun saki layin su, sun shiga harkar siyasa ana amfani dasu wajen cin mutuncin mutane. In Allah ya yarda a wannan kasar tamu za'a sam gyara, sai anyi

ADVERTISEMENT

garambawul ga yan sanda a Kano musamman irin shugabanci da muke gani a Kano da ma wurare da dama a kasar baki daya."

Shi da madugun ya zayyana cewa ya dauki mataki na fasa zuwa jihar Kano bisa ga maganganun da wasu masu fadi-aji suka yi mishi kuma yayi  ala'akari da soyeyyar da yak dashi ga al'ummar jihar wanda baya son wani mugun abu ya faru da su bisa ga mugun nufi da makiyan shi ke kokarin aikatawa akan zuwan shi kano.

Kwankwaso yana mai cewa idan lokacin zuwan shi Kano ayi dole ya tafi domin kuwa komai da lokacin sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT