ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hoton ginin matar tsohon shugaban kasa dake Abuja da gwamnati ta ruguza

An rusa ginin wanda ke yankin Mabushi na babban birnin tarayya yau Talata 16 ga wata kan laifin ginawa ba tare da an bi tsarin doka.

Ana amfani ginin wajen gudanar da ayyukan gidauniya wanda ita Patience Jonathan ta bude.

Game da rusawar alkalin uwargidan tsohon shugaban kasa Emmanuel Anene yana mai cewa abun ya bashi mamaki ganin yadda hukumar FCDA ta rusa gini duk da cewa an nuna masu tsarin yadda aka gina ta cikin ka'ida.

Alkalin ya kara da cewa an kai karar  hukumar kotu kan laifin yin watsi da tsarin doka tare da ruguza ginin ba tare da an bi tsarin doka ba.

Yace hukumar ta fada ma ginin kwatsam ba tare da ta bayar da wata tsammaci ko sanarwa kafin su hakan.

ADVERTISEMENT

Hukumar FCDA ta  musanta wannan zargin da alkalin yake inda tace ta fitar da sanarwa kafin su far ma ginin wanda aka gina ba tare da ta samu izini.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT