ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mukaddashin shugaban kasa yayi Allah wadai game da matan da aka sata

Osinbajo ya jajanta ma dangin matan wadanda yan boko haram suka sata a jihar Borno

Professor Yemi Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi Allah wadai game da matan da yan ta’adda suka sata a jihar Borno kuma ya bada tabbaci cewa gwamnatin tarayya zata iya bakin kokarin ta don ganin sun dawo ga dangin cikin koshin lafiya

A wani litafi da mai magana da yawun mukaddashin Laolu Akande ya fitar ranar laraba 19 ga watan Yuli a garin Abuja mukaddashin yana ma dangin matan jaje.

Ya umurci sojoji na kasa da sauran ƙungiyoyin basira da su dauki duk wani mataki da ya kamata wajen ganin cewa matan sun dawo in son samu ne su hada gwiwa da sauran ƙungiyoyi na kasashen waje

Osinbajo ya yi umurci jami’an tsaro da su karfafa tsaro a yankin jihar Borno.

ADVERTISEMENT

A karshe mukaddashin ya jajirta wa hukumomin tsaro na kasa a kan rawan da suke takawa wajen magance ta’addanci a kasar.

A labarin da NAN ta fitar boko haram sun saci matan a ranar litinin kuma sun saki bidiyo mai tabbatar da haka.

sun saci matan yayin da suke zuwa binne wata ma'aikaciyar yan sanda da ta rasu a garin Damboa

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT