Jiya 28 ga watan Yuni 2017 rundunar yan tsaro da bincike sun far wa gidan tsohon shugaban kasa Namadi Sambo dake no.1 Alimi road na kaduna don yin bincike.
Rundunar yan tsaro da bincike sun far wa gidan tsohon shugaban kasa
An samu labari cewa rundunar sunyi bincike a gidan kusan sa’o’i 2 tare da kulle hanyoyi dake kusa da gidan.
Rundunar sun hada da yan sanda da yan sandan farin kaya tare da jagorancin jami’an hukuma mai yaki da laifuffukan cin hanci da rashawa watau ICPC.
An samu labari cewa rundunar sun kaddamar da bincike har sa’o’i 2 tare da kulle duk wani hanya dake kusa da gidan.
An ruwaito cewa rundunar sun gudanar da binciken don gano wasu takardu da kudi wadda ma suka dauki wani mai aikin hannu da ya taimaka masu wajen bude rufin gidan.
Jaridar punch sun ruwaito cewa wannan shine karo na biyar da ake yin bincike a gidan cikin wata 3
Mataimakin Sambo kan watsa labarai, Mallam Umar Sani yace rundunar basu gano komai a binciken da suka yi.
Hukumar yaki da rashawa (EFCC) na gudanar da bincike kan tsohon mataimakin shugaban kasa bisa ga zargin raba wasu kudi kafin a gabatar da zaben shugaban kasa a shekara 2015.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng