Pulse.ng logo
Go

NYSC Matasa masu yi ma kasa hidima 1,596 cikin 2,126 sun bukaci a canza masu jiha a Adamawa

Jami'in dake kula da shirin NYSC a jihar Adamawa yace mafi yawancin matasan da aka turo jihar sun nemi a canza masu jiha

  • Published:
Batch ‘B’ corps members to begin orientation on Tuesday, July 24, 2018 play

Corps members at orientation camp

(PM News)

Matasa na daga cikin masu yi ma kasa hidimi na shirin NYSC sun bukaci a canza masu jiha bisa ga matsalar tsaro.

Cikin su 2,126 da aka turo jihar, mutum 1596 sun nemi a tura su wata jiha banda jihar Adamawa.

Jami'in dake kula da shirin NYSC a jihar Adamawa, Mallam Abubakar, yace mafi yawancin matasan da aka turo jihar sun nemi a canza masu jiha.

Ya kara da cewa, yayin da aka mika ma matasan takarda  bayan horo da aka gudanar ma sabbin shiga shirin, mafi yawanci sun ki amincewa da inda aka tura su domin cigaba da aikin bautar kasa.

Kamar yadda ya sanar, matasan sunki amincewa da cigaba da bautar bisa ga dalilin matsalar tsaro da rashin lafiya da dalilin rayuwar aure.

Sauran matasa 530 da suka amince da cigaba da yin hidima a jihar, Malam Abubakar ya sanar cewa ba'a tura su kananan hukumomi na jihar irin su Michika da Madagali da Mubi da kudu da mubi ta arewa, bisa ga dalilin matsalar tsaro da suke fuskanta.

Yayi kira ga jama'ar jihar da su mara ma matasan da suka amince da yin aiki a jihar baya wajen tafiyar da aikin su yadda ya kamata.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.