ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Matar tsohon gwamnan jihar Adamawa ta rasu

Ta rasu a asibitin tarayya dake nan garin Yola daren ranar laraba bayan rashin lafiya da tayi

Ta rasu a asibitin taraya dake nan garin Yola daren ranar laraba 20 ga watan Yuni bayan gajeruwar rashin lafiya da tayi. Kamar yadda majiya suka shaida, an ruga da ita asibitin ranar talata baya ta yanke jiki ta fadi a gida.

Anyi jana'izar ta a nan garin Dougirei inda gidan mijinta yake. Ta rasu tana da shekaru 63 a duniya.

Ta rasu ta bar mijinta, Murtala Nyako da yara 6 da jikoki 10 tare da mahaifiyar ta.

ADVERTISEMENT

Al'ummar jihar Adamawa sun taya iyalen tsohon gwamna ta'aziya bisa rashin da ya samu. Shima tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya mika sakon ta'aziya ga iyalen.

A wakon da ya wallafa a shafin sa na twiter, Alhaji Atiku Abubakar ya taya iyalen Murtala Nyako jaje a madadin sauran iyalen gidan sa. Yayi mata addu'ar Allah ya sa aljanna ce makomarta.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT