Pulse.ng logo
Go

Labari cikin hotuna Fuskokin jarumai da suka halarci bikin auren Ramadan Booth

Jarumi Ramadan Booth, ya angwance a karshen makon da ya shude ga amaryar sa Fatima Ibrahim.

  • Published:

Fitattun jarumai da masu hannu da shuni na masana'antar fim ta Kannywood suka halarci taronn bikin auren daya daga cikin su.

Jarumi Ramadan Booth, ya angwance a karshen makon da ya shude ga amaryar sa Fatima Ibrahim.

An daura auren su ranar juma'a 30 ga watan Yuni a nan garin Kano. Bayan haka an kuma shirya liyafa ta musamman domin raya auren.

Abokan aikin sa na dandalin nishadantarwa sun halarci taron bikin da ya shirya. Cikin manyan fuskoki na daga cikin  da suka garzaya liyafar akwai Ali Nuhu, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, Garzali Miko, Nazir Danhajiya, mawaki Nazir M.Ahmed da sauran su.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement