Pulse.ng logo
Go

Khadimul Kur'an Shahararen malamin addini kuma hamshakin dan kasuwa, Sheikh Isyaka Rabiu ya rasu

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a 'yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya

  • Published:
Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya play

Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya

(DailyNigerian)

Allah yayi ma sheikh Isyaka Rabiu Rasuwa. Ya rasu a asibiti dake birnin London ranar talata.

Za'ayi jana'izar shi ranar laraba da zaran gawar shi ta dawo Nijeriya.

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a 'yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya.

Marigayin, fitaccen malamin addini ne kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya kafa kamafanin Isyaka Rabiu and Sons.

Ya rasu ya bar mata da yara da jikoki da yawa. Cikin yaran sa akwai Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, shugaban kamfanin BUA da Nafiu Isyaka Rabiu shugaban kamfanin jirgin sama ta IRS.

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Qur'an".

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.