ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

‘Ku ba karatun mata muhimmanci a Nigeria’ inji Malala zuwa ga mukaddashin shugaban kasa

Matashiyar wanda ta shahara wajen kare hakkin mata ta bada wannan shawarar yayin da ta gana da Osinbajo a fadar shugaban kasa

Pakistani Nobel Peace Laureate Malala Yousafzai, pictured on July 10, 2017, visited Nigeria, where she met with the government and asked for serious reforms in the country's education system

Matashiyar wanda ta amshi lambar yabo ta shawarci gwamnatin Nigeria da ta ba karatun mata muhimmanci a lokacin da ta kai wa kasar ziyara inda ma ta gana da wasu daga cikin yan matan chibok da suka kuɓuta.

Yousafzai Malala mai shekara 20 a duniya ta bada wannan shawarar yayin da ta gana da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa .

Nigeria tana da akalla yara miliyan 10.5 wadanda basu samu damar shiga makaranta kuma kaso 60 daga ciki mata ne a bayanin da Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya YUNISEF ta fitar.

YUNISEF tace mafi yawancin yaran suna yankin arewa maso gabas na kasar inda ƙungiyar yan ta’adda boko haram suka gurbatar da tsarin karatun su.

ADVERTISEMENT

Malala wanda ƙungiyar yan ta’adda taliban dake kasar Pakistan suka harba a shekara 2012 don ta tsaya akan batun cewa dole mata su yi karatu ta bayyana ma yan rahoto cewa sun tattauna akan batutuwa da dama tare da Osinbajo.

“Na shawarci gwamnati da ta daura ma karatu muhimmaci don karatun ga yaran Nigeria maza da mata yana da matukar muhimmanci”

Ta kara da cewa akwai ƙamshin jituwa game da shawarar da ta badawa Osinbajo wanda ke maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari tun da ya yi tafiyar rashin lafiya.

Malala wanda ta amshi lambar yabo a shekara 2014 tana daga cikin mutane masu daraja a duniya da suka goyi bayan yin zanga-zanga na ganin cewa a saki yan matan chibok.

A ziyaran da ta kawo ma kasar Nigeria cikin shekara 2014 ta yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kira da ya taimaka ya ziyarci iyayen yan matan.

ADVERTISEMENT

Matashiyar ta kira yan matan yan’uwan ta kuma ta nuna farin ciki da ta gan wasu daga ciki wadanda suka kubuta daga hannun boko haram.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT