Ga wasu daga cikin kanun labarai da suka fito a makon da ya shude.

Shugaba Buhari ya kai ziyara birnin Beijing

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kwana shida zuwa kasar Sin inda ya halarci taron Forum On China-Africa Corporation.

Shugaban ya gana da yan Nijeriya mazaunin kasar yayin ziyarar. Ya tafi ranar 1 ga watan Satumba kana ya dawo gida ranar shida ga wata.

Mallam Ibrahim Shekarau ya fice da PDP

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Mallam Ibrahim Shekarau ya fice daga babban jam'iyar adawa ta PDP bayan zargin rashin adalci da yayi ma jam'iyar na fifita Kwankwaso bayan ta rushe shugabancin jam'iya ta jihar Kano.

Ya koma tsohon jam'iyar sa APC wanda dashi aka gina ta bayan yunkurin da  jiga-jigan jam'iyar suka yi na shawo kanshi.

Tsohon shugaban majalisar Dattawa zai tsaya takarar shugaban kasa

David Mark ya shiga cikin jiga-jigan yan siyasara PDP dake neman haye kujerar shugaban kasa a zaben 2019. Tsohon shugaban majalisar dattawa ya siya fom din takara inda zai fafata da sauran yayan jam'iyar domin zama gwanin jam'iyar da zai wakilci ta a zaben shekarar mai zuwa.

NFF ta dakatar da Salisu Yusuf

Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF ta dakatar da kocin tawagar yan wasan super eagles bayan ta kama shi da laifin karbar cin hanci don saka sunan yan wasa cikin tawagar yan kwallon Nijeriya.

Ya samu hukun dakatarwa na tsawon shekara daya tare da biyan tara na dala dubu biyar ($5,000) bayan bincike da kwamiti na musamman da hukumar ta kafa wanda tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu ya jagoranta.

Kungiya ta siya ma shugaban fom din tsayawa takara

Wata kungiya mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network ta mika kudin (N45M) na fom din takarar shugaban a hedkwatar jam'iyar APC dake nan Abuja.

Sanusi ya shaida cewa ya'yan kungiyar tunda daga karkara da kananan hukumomi na jihohin kasa suka hada kudin siyan takardar domin nuna gamsuwar su ga shugabancin shugaba Buhari.

Kungiyar tace ta amince da mulkin shugaban wanda ya sanar da anniyar sa na zarcewa kan karagar mulki.

Adam Zango ya nemi afuwar Ali Nuhu

Jarumi ya nemi gafarar tsohon aminin sa a cikin wani sako da ya wallagfa a shafin sa na Instagram wanda ya wallafa hoton su tare inda ya durkusa a kasa yayin da shi Ali Nuhu ke saman kujera.

Tawagar super eagles ta lallasa Seychelles 3-0

A wasan neman shiga gasar kofin Afrika wanda tawagar yan kwallon Nijeriya suka yi da Seychelles, Nijeriya tayi nasarar lallasa abokan adawar su.

Ahmed Musa ya fara zura kwallo a raga cikin minti sha biyar da fara wasan wanda aka aka tashi 3-0.

Chigozie Awaziem da Odion Ighalo suka kara ma Nijeriya.