Pulse.ng logo
Go

Maina Maina ya maka hukumar EFCC da Interpol kotu kan tallata shi da suka yi

Maina ya nemi a biya shi diyar miliyan N500 a matsayin kudin fansa na barnar da aka aikata wanda ya sabawa yancin shi.

  • Published:
Maina sues AGF, EFCC, INTERPOL for being declared wanted play

Abdulrasheed Maina

(File)

Tsohon shugaban kwamitin gyaran fuska na hukumar fansho Abdulrasheed Maina yayi fito-na-fito da hukumomi a gaban kotu kan gabatar dashi a matsayi wanda ake nema ruwa a jallo.

A karar da aka shigar wanda ke dauke da rijistar FHC/ABJ/CS/1174/2017, Maina ya musanta tare da yin la'akari da wata sanarwa wanda aka wallafa a jarida ranar 7 ga watan Nuwamba na 2017 inda aka kaddamar dashi a matsayin wanda hukuma ke nema ruwa a jallo, yana mai cewa wannan ya sabawa yanci shi wajen kare martaban shi.

Tsohon shugaban kwamintin gyaran fuska na hukumar fansho Abdulrasheed Maina play

Tsohon shugaban kwamintin gyaran fuska na hukumar fansho Abdulrasheed Maina

 

Ana ta kai-kawo da tsohon jami'ihukumar fansho ne bayan dawowar shi aiki cikin bara duk da cewa ana zargin shi da aikata laifin almundahana wanda har sanadiyar hakan ta tsere daga kasar a tsawon shekara biyu.

*Abdulrasheed Maina wanda hukuma ke nema ruwa a jallo yanada katin kasa na kasar Amurka banda ta Nijeriya

Hukumar dake yaki da masu yi ma dukiya zagon kasa ta EFCC ta zargi Maina da satar naira biliyan 2.1 na hukumar fansho cikin 2013. Bayan haka an salame shi daga aiki har ma EFCC ta kaddamar dashi a matsayin wanda ake nema ido rufe.

Bayan tirka-tirkan da yafaru sandiyar dawowar shi aiki bara, hukumar ta kara kaddamar dashi a matsayin mai laifi wanda hukuma ke nema, bisa ga wannan yunkurin hukumar ta tallata hoton sa a jarida wanda aka wallafa ranar 7 ga wata nuwamba na 2017.

A karar da aka shigar, maina yace EFCC da hukumar yan sanda na kasa da kasa da dai sauran hukumomi sun keta hakkin sa tare da takura ma hakkin shi sanadiyar barazanar da suka yi na kama shi. yace yin haka ya tauye hakkin shi na samun yancin walwala da samun saurara da ya dace kuma cikin adalci.

Bukatar Maina ga kotu

Maina ya nemi a biya shi diyar miliyan N500 a matsayi fansa na barnar da aka aikata wanda ya sabawa yancin shi.

Ya nemi kotu da ta aiwatar da hukunci da zai hana hukumomi wajen cin zarafin shi da kuma gurfanar dashi daga hannun hukumomin.

*Bidiyon Maina yayin da yake neman shugaba Buhari da ya saurare shi domin wanzar da zargin da ake mashi

Hakazalika ya nemi hukumar EFCC da ta nemi gafara a hannun shi ta hanyar wallafa sakon yin haka a jaridu 3 bisa tallar da suka yi kwanan baya na kaddamar dashi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Ya shigar da karar zuwa ga ministan sharia Abubakar Malami da hukumar EFCC har zuwa ga babban sufeton yan sanda na kasa Ibrahim Idris da Interpol da ma'aikatae hukumar shige da fice.

Alkalin Maina wanda ya gabatar da karar O.J. Onyemah yana mai cewa babu dokar data ba hukuma damar kaddamar da shi a matsayi mai babban laifi.

Ya kara jaddada cewa doka bata basu damar tallata Maina a jarida a matsayin 'Mai laifi' tare da wallafa hoton shi bayan kotu bata saurari zargin da ake yi kan shi balle ta yanke masa hukunci ba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement