Yan sanda sun kama wata tsohuwa mai shekara 92 da ta  kashe danta mai shekara 72 da bindiga hayan ya nemi ya kai ta gidan kula da tsofaffi.

Anna Mae Blessing,ta shiga hannun yan sanda Amurka inda ake tuhuma da kisan gilla don nuna rashin jin dadinta game da aniyar danta.

Kamar yadda takardun da aka gabatar a gaban kotu suka bayyana tsohuwar ta bayyana ma dan cewa bata son tafiya gidan.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar 2 ga watan Yuli a g arin Fountain Hills da ke karamar hukumar Maricopa, kamar yadda kafofin watsa labarai na garin suka ruwaito.

"Ka raba ni da raina, a kan haka zan dauki naka," haka rahotanni suka ruwaito tsohuwar na cewa lokacin da 'yan sanda suka zo gidan da take zaune da danta da buduwarsa a nan Arizona.

Dan Misis Blessing, wanda ba a bayanna sunansa ba ya so ta koma gidan kula da tsofaffi saboda babu "jituwa" tsakaninsu.

Yan sanda sun ce mahaifyar mutumin ta boye bindigogi biyu a cikin rigarta kafin ta tunkari danta a cikin dakinsa.

A lokacin da gardama ta kaure tsakaninsu, ta fitar da daya daga cikin bindigogin da ke hannunta, wadda ta saya a shekarar 1970 kuma ta harbe shi.

Misis Blessing ta kuma nuna wa buduwar danta mai shekara 57 bindiga, wadda ta kwace bindigar daga hannunta ta jefar a wani bangare na dakin.

Sai kuma ta fitar da bindiga ta biyu, wadda ta fada wa 'yan sanda cewa mijinta da ya rasu ne ya ba ta a shekarar 1970.

Sai dai budurwar ta kabe bindigar daga hannun Misis Blessing kafin ta tsere kuma ta kira ofishin 'yan sanda.

Yan sanda sun gano Misis Blessing kan wata kujera da ke dakinta. Daga bisani ta fada mu su cewa ya kamata "a sata ta yi barci" saboda abin da ta yi.

Ana zarginta da kisan gilla da sace mutum, kuma za ta biya dala 500,000 a matsayin beli.