ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mai ya sa sufeton yan sanda ya gagara furta kalamai?(Bidiyo)

Shugaban rundunar yan sandan Nijeriya ya gagara furta wasu kalamai yayin da yake jawabi a wani taro.

Lamarin ya faru ranar litinin a garin Kano yayin da ya je kaddamar da wani cibiyar hukumar yan sanda.

Bidiyon dai ya janyo cece-kuce a shafukar kafafen watsa labarai. Jama'a na ta mamakin yadda kalaman suka gagari jami'in dan sanda.

Sa-in-sa tsakanin majalisa tarayya da sufeton yan sanda

ADVERTISEMENT

Sau uku majalisar ta gayyace shi zauren su domin bada amsar tambayoyi game da matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar da tuhuma da dan majalisa dattawa, Dino Melaye.

Shi dai jagoran yan sanda ya ki amincewa da gayatar a duk lokutan da suka gayyace shi.

Dangane da jayayya dake faruwa tsakanin su, majalisar ta kira sufeton a matsayin makiyin tsarin dimokradiya.

Kan batun gayyatar, shima sufeton yan sanda ya mayar da martani ga majalisar dattawa game da kalaman shugaban ta na cewa bai cancanci rike mukami a kasar ba.

ADVERTISEMENT

Ibrahim Idris yayi karin haske kan rashin kin amince da gayyatar da aka yi masa, yace yan majalisar na neman ci masa fuska domin canza alkiblar sa wajen tabbatar da shari'a.

Yace gayatar manufa ce na ci masa fuska tare da bata masa suna kan tagomashi dake tsakanin yan sanda da sanata Dino Melaye.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT