ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Rahama Sadau tayi nadamar abun da ya faru baya, ta baiwa kowa hakuri

Jaruman ta bada hakurin a wata wasika da ta tura ma kungiyar MOPPAN

Bayan kusan shekara daya da aka dakatar da ita jarumar masana'antar shirya fina-finai hausa Rahama Sadau ta bada hakuri game da abun da yayi sanadiyar dakatar da ita a masana'antar.

Jarumar ta bada hakuri ga gwamnatin jihar Kano da mai martaba sarkin Kano  da kungiyar masu shirya fina-finan hausa na MOPPAN.

MOPPAN cikin watan octoba na bara ta kori jarumar cikin gaggawa daga Kannywood bayan wata bidiyo da take runguma tare da yin kwanciya a jikin mawaki Classiq a cikin wani wakar sa ya yadu wanda yin haka ya sabawa dokar yan wasan kannywood.

Banda wasikar jarumar ta kara bada hakuri ga gwamnan jihar kano da mai martaba sarkin kano da mabiyan fina-finan kannywood ne a wata hira ta musamman da tayi a shirin "ku karkade kunnuwan ku" wanda gidan rediyo na Rahama dake nan jihar Kano ke gabatarwa.

ADVERTISEMENT

A hira Rahama tayi nadamar abun da ya faru kuma ta baiwa jama'a tare da shugabannin kannywood hakuri game da tsegumin da lamarin ya janyo.

"Ni halittar Allah ce wanda za ta iya aikata kuskure ko yaushe sannan kuma ni ‘ya ce mai laifi wanda ke shirin gyara abubuwan da nayi ba daidai ba. Ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu MOPPAN, da da masoya na da suyi hakuri da ni su yafe min" ta rubuta a wasikar da ta tura ma MOPPAN.

Sakatarren kungiyar Muhammad Salisu ya tabbatar da isowar wasikar ga kungiyar inda ya kara da cewa kungiyar zata zauna domin tsayar da matsaya akan batun.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT