ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnati tana tattaunawa da Boko haram kan tsagaita bude wuta

A wata ganawa ta musamman da yayi da manema labarai a jihar Legas ministan yayi karin hasken kan yadda aka saki yan matan Dapchi

A wata ganawa ta musamman da yayi da manema labarai a jihar Legas ministan yayi karin hasken kan yadda aka saki yan matan Dapchi.

A cewar shi, tun ba yau ba gwamnati ke tattaunawa da yan ta'addar kan matakin tsagaita bude wuta kan ayyukan ta'adanci.

Yace sakamakon tattaunawan dasu suka yi aka nasarar sakin malaman jami'an maiduguri da matan yan sanda da aka yi kwanan baya.

Haka zalika yarjejeniyar dake gudana tsakanin su da mayakan yayi sanadaiyar sakin yan matan Dapchi.

ADVERTISEMENT

Ministan yace yan ta'adar sun bukaci gwamnati da ta tabbatar da  ta samad  da hanya ba tare da fargaban jami'an tsaro ba domin mayar da yan matan cikin ruwan sanyi.

Ministan yace kan wannan bukatan aka aminci da yan ta'adar da wajen tsagaita da bude wuta tun daga ranar 19 ga watan Maris.

Lai Muhammed yayi karin haske tsabanin jita-jita da jama'a keyi kan yadda mayakan boko haram suka dawo da yan matan cikin ruwan sanyi ba tare da fuskantar barazana daga jami'an sojoji.

Ya kuma jaddada cewa gwamnati bata biya kudin fansa ba kuma bata yi musanya da yan kungiyar da aka garkame domin sakin yan matan.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT