Fitattun jarumai da masu hannu da shuni na masanaantar fim ta Kannywood suka halarci taronn bikin auren daya daga cikin su.

Jarumi Ramadan Booth, ya angwance a karshen makon da ya shude ga amaryar sa Fatima Ibrahim.

An daura auren su ranar juma'a 30 ga watan Yuni a nan garin Kano. Bayan haka an kuma shirya liyafa ta musamman domin raya auren.

Abokan aikin sa na dandalin nishadantarwa sun halarci taron bikin da ya shirya. Cikin manyan fuskoki na daga cikin  da suka garzaya liyafar akwai Ali Nuhu, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, Garzali Miko, Nazir Danhajiya, mawaki Nazir M.Ahmed da sauran su.