ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya ta saki biliyan N243 ma jihohin kasa

jihar Bayelsa, Rivers, akwa ibom, Delta da Kano sun samu kaso mafi tsoka, ko wanne ta samu naira biliyan goma (N10bn)

Gwamnatin tarayya ta saki jimillar naira biliyan 243 ma jihohi 36 dake kasar harda birnin taraya

A bayanin da ministn kudi Kemi Adeosun ta fitar, an saki kudin bayan amincewar da Shugaba Muhammadu Buhari yayi a watan Mayu.

Yayin tattaunawa akan kudin, Adeosun tace an biya kudin ne don yarjejeniya da aka yi da gwamnonin jihohi wadanda ke inƙari cewa ana cire kudi daga asusun tarayya domin biyan basussuka da aka ciyo tsakanin shekara 1999 da 2002.

“An saki kudin don tada komadar tattalin arzikin kasa musamman domin tamakawa jihohi wajen biyan albashi da sauran aikace-aikacen jihohin. Wannan zai magance ƙalubalen da ma’aikata ke fuskanta” inji ministan.

ADVERTISEMENT

Cikin kudin da aka saki jihar Akwai ibom, Delta, Cross river, Bayelsa da Kano suka samu kaso mafi tsoka ko wanen su ta samu naira biliyan 10.

Jihar Gombe, Ekiti, Ebonyi da nasarawa suka samu kaso mafi karanci inda ko wannen su ta samu naira biliyan 4.

A samu jayayya sanadiyar biya ta farko da gwamnatin tarayya ta yi na naira biliyan N522.74 inda aka zargi wasu gwamnoni da kashe kuɗin a kan wata manufa daban.

Labari ya nuna cewa a watan febreru da ya gabata hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC tana tuhumar wasu gwamnoni 7 bisa ga zargin juwa akallar kuɗi zuwa wata manufa daban.

Ciki akwai shugaban majalisar gwamnoni na kasa gwamna Abdul’aziz Yari na jihar wanda ake zargi da satar naira miliyan N500

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT