ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Bayan yan kwanaki da zama a gidan yari, kotu ta ba tsohon gwamna damar yin beli

Kotu ta bashi damar yin beli da naira miliyan 100 tare da matakin gabatar da shaidu guda da zasu tsaya a madadin shi.

TSohon gwaman kuma dan majalisar dattawa, ya shiga hannun hukuma tare da wani ma'aikacin gwamnatin sa sanda yake gwamna mai suna Yusuf Pam, kan zargin da EFCC ta shigar na yin awon gaba da kudin da babban bankin Nijeriya ta tura jihar Filato.

A zaman kotu da aka yi yau alhamis 24  ga watan Mayu, mai shari'a Daniel Longji ya basu damar yin beli.

Game hukuncin Pam, kotu ta bada damar yin beli matukar ya gabatar da shaidu biyu tare da biyan naira miliyan 50.

Tsare shi a kurkuku

ADVERTISEMENT

A makon da ya gabata Babban kotu dake zaman ta a jihar Filato ta bada damar a cigaba da garkame tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang a gidan kaso.

Kotun ta bada umarnin cigaba da tsaran shi har zuwa ranar 24 ga watan Mayu bisa karar laifin wawure kudin jihar da aka shigar.

A zaman kotu da aka yi ranar laraba 16 ga wata, mai shari'a Daniel Longji ya ki amincewa da bukatar belin da tsohon gwamnan ya nema a daga ranar zantar da hukunci har sai bayan ya gama nazari kan karar shi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT