Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon domin sa hannu ga kasafin kudi na bana.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da hadimin sa, Femi Adeshina, ya fitar wa manema labarai makon da ya gabata.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaban zai sa hannu ga kasafin ranar Laraba 20 ga watan Yuni.

Tun a cikin watan Mayu majalisa dokoki ta tura kundin kasafin zuwa ga shugaban bayan da yan majalisar suka sa hannu.

Asali, tun a cikin shekarar 2017 shugaban ya mika kasafin kudi na tiriliyan N8.612, sai dai yan majalisar sun kara kudin da biliyan N508 inda daga bayan adadin kudin ya tashi a kan tiriliyan N9.12.

Yayin mika kasafin, shugaban ya bayyana cewa kasafin na bana zai fi na bara kuma ana kyautata zato bana za'a samu kyawawan ayyuka.