Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wannan matakin a wajen taron kaddamar da wani sabon shirin fim da gwamnatin sa ta mara kma baya mai taken "Mutum da addinin sa".
A wajen taron wanda aka shirya a yammacin ranar Asabar 18 ga wata, gwamnan yace manufar yin haka shine domin karfafa gwiwar masana'antar wasan kwaikwayo wajen samad da ayyukan yi da kawar da talauci a cikin al'umma.
Ganduje ya kara da cewa hakan zata taimaka wajen wayar da kawuna tare da bunkasa walwala tsakanin jama'a.
Gwamnan ya kuma sanar cewa gwamnatin sa ta kirkiro wata sabon cibiya mai suna Kannywood development Intiative domin jawo hankulan yan kasuwa na gida da waje wajen zuba jari domin bunkasa masana'antar.
Dakta Abdullahi Ganduje ya kara da cewa cikin tallafin da gwamnatin sa ta baiwa masana'antar shine horas da ma'aikata 450 wajen koya ilimin harkar fim a fannoni daban daban. Hakalizaka gwamnatin sa ta taimaki masana'antar da babura tare da samad da cibiyoyin fim a dukannin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano.
Banda haka, gwwamnatin jihar ta tallafa wa wuraren kallon fina-finai sama da 520 dake jihar da na'urorin zamanin kallo.
Gwamnan yayi kira ga jami'an masana'antar da su biya sakayyar da gwamnati tayi masu ta hanyar fitar da fina-finai masu kunshe da darasi da bunkasa al'adda.
Bugu da kari gwamnan yayi kira na masana'antar tayi bakin kokarin ta wajen daga martabar al'adar gargajiya tare da wanke kanta daga bata gari dake yi ma masana'antar zagon kasa.
Bikin kaddamar da shirin fim ya samu halarcin manyan jami'an gwamnati da ma'aikata da dama da masu ruwa da tsaki a farfajiyar Kannywood.
Bayan ga bakin gida manya baki daga kasar waje sun halarci taron bikin.
Shahararren jarumi Ali Nuhu ya mika wa gwamnan Kano lambar yabo na musamman a taron bisa gudunmawar da yake baiwa masana'antar a madadin sauran ma'aikatan dandalin.
Shirin "mutum da addinin sa"
"Mutum da addinin sa" shiri ne wanda kamfanin Salisu Chali Enterprise ta shirya kuma shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki ya dauki nauyin ta.
Shirin ya yi tsokaci ne kan muhimmancin zaman lafiya,sannan yayi nuni cikin nishadi kan bukatar zama da juna da nuna kauna a cikin al'umma ba tare da la'akari da bambamcin addini ko al'ada ba.
Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin bikin kaddamarwa wanda aka shirya a babban dakin taro na fadar gidan gwamnati.