ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan sanda ya kashe babban dan shi kan zargin sace N2000

Labari ya nuna cewa shi mahaifin ya bine gawar danshi a makabartar Apapa bayan asibiti ta kaddamar dashi a matsayin mamaci.

Ana tuhumar Wani jami'in dan sanda sajent Oludele Olosunde kan kashe dan cikin shi wanda ya zarga da satar naira dubu biyu(N2000).

Mummunar lamarin ya faru ne a unguwar su dake nan unguwar Rasak Okunola Avenue nan garin Ijegun dake jihar Legas wanda bayan haka aka kama dan sanda wanda ke tare da jami'an rundunar yankin kirikiri, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito rahoton.

Bisa ga labarin jaridar Punch dan mai shekaru 17 yana shirin komawa makarantar jami'ar Olabisi Onabanjo ranar litinin 8 ga watan janairu bayan sunan shi ya shiga cikin jerin sabbin dalibai da makarantar ta dauka.

An kama Olusunde ta hanyar wani mazaunin unguwar inda marigayin ya gamu da ajalin shi sanadiyar mahaifin shi. A da dai mahaifin na neman wanzar da kanshi da aikata laifin.

ADVERTISEMENT

"Shine babba cikin yara hudu. mahaifiyar shi bata nan sanda lamarin ya faru, ina ganin tayi yafiya. mahaifin yace yana neman N2000 kuma yana zargin danshi da daukar ta amma dan ya musanta zargin.

"A yammacin ranar bayan ya dawo daga aiki, sai ya hadu da dan a wajen gidansu, nan take ya cafke shi har ya kai cikin gida kana ya tsare shi da tambayar inda kuden shi yake. Dan ya nuna ma uban cewa bai san inda kudin yake ba sai uban ya haushi da duka wanda tsananin shi ya sanya dan ya fita ayacin shi.

"Bayan ya tabbatar da mutuwar shi, jami'in dan sandan ya tafi da gawar har ma ya binne shi amma sai da na kira yan sanda game da laifin da ya aikata" bayanin da shaidar yayi ma wakilin Punch kenan yayin da suka gana.

Kakakin yan sanda na jihar Legas Sp Chike Oki ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin ya kara da cewa ana gudanar da bincike kan lamarin kana ya daura da cewa marigayin ya mutu ne sanadiyar buga kai da yayi a tankin ruwa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT