ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wadanda suka kashe dan uwan mahaifin ministan mai sun samu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Sun kashe marigayin a gonar shi dake karamar hukumar Anioncha kana suka tsere da motar shi kirar KIA Rio

A bisa rahoton da jaridar Guardian ta fitar masu laifin Sunday Luka mai shekaru 32 da Danjuma Kaika mai shekaru 37 da Luka Agu mai shekaru 33 duk yan jihar Nasarawa ne.

Sun kashe kawun ministan mai a gonar shi ranar 9 ga watan Yuni na 2014 a garin Onicha-Ugbo dake karamar hukumar Aniocha nan jihar Delta.

Labari ya nuna cewa masu laifin wadanda asali yan aikin kwadago ne a gonar marigayin, sun kashe shi ne a gonar shi kana suka saci motar shi kirar KIA Rio.

Bayan bincike da hukumar yan sanda suka gabatar aka gurfanar dasu gaban kotu inda aka yi la'akari da kundin tsarin dokokin domin auna nauyin laifin da suka aikata.

ADVERTISEMENT

Bayan kai-kawo da aka na sauraron kara mai shari'a Ogisi ya zantar da hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifufukar da ya danganci kisa da aka kama su da yi.

Mai shari'a yace hukuncin ya zama dole bisa nauyin laifin da suka aikata.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT