Kwana daya bayan fitowar labari takarar majalisar dattawa duk da cewa yana garkame a gidan kaso, jamiyar APC ta mayar da martani game da takarar Joshua Dariye.

A ciki wata takardar sanarwa da kakakin jam'iyar APC Yekini Nebena ya fitar ranar Talata 11 ga watan Satumba, jam'iyar tace baza da yarda tsohon gwamnan ya fito takara ba.

Jam'iyar ta dau wannan matakin ne bayan labari da ya fito cewa Dariye ya siya fom din neman takara ranar litinin kuma har ya cike ta.

Game da faruwar hakan kakakin jam'iyar yace baya da masani ko tsohon gwamnan ya siya fom din kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Yace ya duba cikin sunayen masu neman takarar jihar Filato amma bai gan sunan dariye ba sai dai idan har wasu ne suka siya masa fom din da wata suna daban. Ya kara da cewa idan har haka ne toh jam'iyar zata zare sunan sa domin doka bata yarda wanda yake tsaro a gidan yari ya fito takara.

Tsohon gwamnan jihar Filato wanda yayi wa'adi biyu yana jagorantar al'ummar jihar ya samu hukuncin dauri a gidan kaso na tsawon shekaru sha hudu bayan da aka kama shi da laifin kartata kudin jihar.

Mai sharia Adebukola Banjoko na babban kotu tarayya dake Abuja ya zartar da hukuncin a cikin watan Yuni na 2018.