Jagoran yan wasan tawagar super eagles ta Nijeriya, Mikel Obi, ya mika godiyan sa ga jamian tsaro da suka kubutar da mahaifin shi daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace shi.

Kamar yadda dan wasan ya bayyana, labarin sace mahaifin shi ya kai ga kunnen shi sa'o'i gabanin wasan Nijeriya da Argentina a gasar kofin duniya.

Rahotannin sun nuna cewa an sace mahaifin sa ne hanyar sa zuwa jihar Enugu dake kudancin Nijeriya.

A wata takardar sanarwa da rundunar yan sanda ta jihar Enugu ta fitar, jami'an rundunar sunyi nasarar kubutar da mahaifin dan wasan ranar 2 ga watan Yuli daidai karfe 2 na rana.

Sakamakon kokarin da rundunar yan sanda suka yi, Mikel Obi ya jinjina masu tare da yi masu godiya.

Ga sakon da ya rubuta a shafin sa na twitter kamar haka "Ina mai mika godiya ga jami'an tsaro da suka kubutar da mahaifina bayan lamarin da ya faru cikin satin nan".

Bugu da kari tsohon dan wasan tawagar kungiyar Chelsea dake Ingila, ya yi dinbim yan kasa da suka taya shi jaje tare da mara masa baya.

Lamarin dai shine karo na biyu da masu garkuwa da mutane suka saci mahaifin shahararren dan kwallon. Karo na farko ya faru a cikin shekarar 2011.

Tuni dai dan wasan ke ta samu jinjina da yabo daga yan kasa a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labari bisa bajinta da ya nuna wasan Nijeriya da Argentina duk da ya san cewa anyi awon gaba da mahaifin shi.