Pulse.ng logo
Go

A jihar Kaduna Jirgin kasa ya halaka shanu 53

Lamarin ya faru yayin da makiyayi dake kiwon su ke hanyar sa zuwa jihar Katsina duk cikin aikin kiwo.

  • Published:
A Dutch company, Cownexxion has indicated interest in building cattle ranches in Nigeria. play Makiyayi yana kiwon shanun sa (Punch)

Jirgin kasa dake safara tsakanin garin Kaduna zuwa Abuja ta halaka shanu 53 sakamakon hatsarin da ya faru ranar lahadi 9 ga wata.

Kwamishnan yan sanda na jihar Kaduna Ahmad Abdulrahman ya sanar cewa lamarin ya faru ne a garin Kasarami dake karamar hukumar Kagarko na jihar.

A cewar makiyayin dake kiwon shanun ya fita da su ne bayan ya samu labarin karya cewa jirgin bata aiki ranar lahadi.

Ya kara da cewa lamarin ya faru yayin da makiyayi dake kiwon su ke hanyar sa zuwa jihar Katsina duk cikin aikin kiwo.

Kamar yadda ya bayyana jama'ar garin sun firgita domin suna zaton cewa yan ta'adda ne suka kawo farmaki.

Kwamishnan yace kwantar da hankulan jama'a tare da jaddada cewa babu wani ran dan Adam da aka rasa kana yace rundunar yan sanda zata cigaba da iya bakin kokarin ta wajen tabbatar da zaman  lafiya a yankin.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement