Pulse.ng logo
Go

Rasuwar Khalifa Isyaka Rabiu Jihar Kano ta kaddamar da ranar Juma'a a matsayin ranar hutu

Ana sa ran cewa, gawar shi zata iso Nijeriya ranar alhamis kana za'ayi jana'zar sa a nan garin Kano da misalin karfe 2:30 na ranar Juma'a.

  • Published:
EFCC denies receiving N10m from Gov Ganduje play

Gov. Abdullahi Ganduje of Kano State

(Punch)

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ranar juma'a 11 ga wata a matasayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar.

Wannan labarinya fito ne a wata sanarawa da kwamishnan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba, ya fitar wa manema labarai ranar laraba 9 ga watan Mayu.

Kamar ya yadda sanarwa ta bayyanar, gwamnatin ta bada hutun ne domin ma'aikatan jihar sun halarci jana'izar babban malamin addini, Sheikh Isyaka Rabiu  wanda ya rasu ranar talata.

Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya play

Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya

(DailyNigerian)

 

Marigayin ya rasu a asibiti dake birnin London bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Ana sa ran cewa, gawar shi zata iso Nijeriya ranar alhamis kana za'ayi jana'zar sa a nan garin Kano da misalin karfe 2:30 na ranar Juma'a.

Labarin rayuwar sa

Marigayin, fitaccen malamin addini ne kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya kafa kamafanin Isyaka Rabiu and Sons.

Cikin yaran sa akwai Nafiu Isyaka Rabiu da Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, shugaban kamfanin BUA da Nafiu Isyaka Rabiu shugaban kamfanin jirgin sama ta IRS.

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Qur'an".

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement