An samu labarin jarumin magidanci da yayo kokawa da barayin da suka far ma gidan sa a jihar NIger duk da raunin harbin bindiga da ya samu.

A labarin da jaridar Punch ta fitar, rundunra yan sandan jihar sun kama barayin, Isah Kabiru da Abdullahi Musa bayan arangamar da ya faru a gidan Gado Aliyu.

Wakilin rundunar yan sanda, Muhammed Abubakar, yace ana daf da gurfanar da barayin gaban kotu domin fuskantar hukuncin doka kan laifin da ake zargi sun aikata.

Kamar yadda wakilin ya bayyana ma Northern City News, daya daga cikin barayin mai suna Sanda Chumo, ya tsare yayin da jami'an tsaro suka yunkura wajen kama su.