ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

“Maganin gargajiya kadai ke iya warkar da shugaban kasa” - inji masu maganin gargajiya

Ƙungiyar masu maganin gargajiya sun fitar da hanya da shugaban kasa zai bi don samun lafiya

President Muhammadu Buhari

Ƙungiyar masu maganin gargajiya sunyi kira ga fadar shugaban kasa da su yi maza-maza su dawo da shugaba Muhammadu Buhari daga kasar Ingila don suna da maganin da zai warkar da ciwon shi.

A bayanin da yayi cikin wani hira ta musamman jagoran ƙ bungiyar Dr.Adesunmiboye Fawawo yaceduk wani cuta da shugaba buhari ke fama dashi masu maganin gargajiya na iya warkar da ita indai zai nemi su.

A inda yake wannan bayanin Dr. Fawawo yace mafi yawancin yan nijeriya sun raina maganin gargajiya shiyasa yawanci suke mutuwar bazata don ba’a san muhimmancin maganin ya’yan itatuwa ga lafiyar jiki.

“Shugaba Muhammadu Buhari jagoran kasar mu ne kuma dole mu kare shi ta ko wani hanya da muke iyawa. An san da zaman kungiyar mu a fadin kasar.

ADVERTISEMENT

“An kafa ƙungiyar a mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kuma shi Obasanjo na shan magungunan mu. Shiyasa har yanzu da karfin shi duk da yawan shekarun shi.

“Mun sha warkar da mutane wanda harma iyalin su sun cire rai cewa zasu samu sauki. Abun taƙaici ne da ba’a nemi mu don samar ma Shugaba Buhari magani. Muna ita warkar dashi kuma ina son gwamnati ta gane cewa ba lalle bane a samu magani da zai warakar dashi a can kasar waje”

“Idan ka ziyarci makabarta zaka gan cewa mafi yawancin gawawaki dake ciki na masu kudi ne don basu yarda da maganin gargajiya. Mafi yawanci masu kudi sun fiye amfani da magungunar kimiyya masu tsada kuma aikata haka na haddasa koma bayan tattalin arzikin kasa” Dr. Fawawo yace.

Jagoran kungiyar ya kara da cewa masu korafin cewa maganin gargajiya na haifar da wasu cututuka kamar ciwon koda da sauran su, na tsorartar da sauran jama’a. Ta jaddada cewa idan fadar shugaban kasa ta nemi su hakika zasu nema ma shugaba maganin da zai warkar da ciwon shi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT