Pulse.ng logo
Go

Hotuna daga bikin karramawa da Aisha buhari tayi ma yan Kannywood

Gidauniyar ta ta shirya taron karramawa a dakin taro na fadar shugaban kasa yayin kaddamar da sabuwar waka da jaruman suka shirya mai taken 'sakamakon canji'.

  • Published:
play (Instagram/buharisallau)

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta karrama wasu daga cikin fitattun jaruman masana'antar nishadi ta kannywood mawaka da yan wasan kaikwayo.

Gidauniyar ta ta shirya taron karramawa a dakin taro na fadar shugaban kasa yayin kaddamar da sabuwar waka da jaruman suka shirya mai taken 'sakamakon canji'.

play (Instagram/buharisallau)
play (Instagram/buharisallau)


 

Shahararren mawaki Abdul Amart tare da wasu mawakan Hausa suka shirya wakar 'Sakamakon canji' mai bayyana ayyukan cigaba da gwamantin buhari ta aiwatar a wa'adan sa na farko da yin mulki.

play (Instagram/buharisallau)

 

Aisha Buhari ta jinjina ma jaruman masana'antar nishadi ta Kannywood bisa ga gudummawar da suke bada wa wajen wayar da kan al'umma tare da haifar da zaman lafiya.

Ta ce ya zama dole a karramar jarumai domin rawar da suke takawa wajen cigaban gwamnati baya misaltuwa.

play (Instagram/buharisallau)

 

Taron dai ya samu halarcin shugaba Muhammadu Buhari tare da wasu manyan ma'aikatan fadar sa.

Fiattun mawaka da suka halarci taron sun hada da Naziru M.Ahmad, Aminu Ladan Abubakar (Alan waka), El-Muaz, Ado Gwanja, Nazifi Asnanic, Ali Jita, Fati nijar da sauran su.

play (Instagram/buharisallau)

 

play (Instagram/buharisallau)

 

A bangaren jaruman fim kuwa akwai  Adam A.Zango, Fati Washa, Rukayya Dawayya, Jamila umar Nagudu, Maryam Yahaya, Halima Atete, Hauwa Waraka, Fati S.U, Dan Auta, Aminu Saira, Amal Umar da Fati Shu'uma.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement