ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ƴarinyâ mai shekâra gomâ sha ukkù ta mutu domin azumi na kwana sitttin da takwas

ʼƳar-indiya mai shekâra goma sha ukkù daga garin Hyderabad, tá mutu bayan azumi na kwana sitttin da takwas wajen bautaʼn gunkiʼn Jain, a cikin watan tsalki mai suna "Chaumasa".

The deceased, Aradhana

Mutanen da suka kawo gaisuwa wajen janaʼizar, sun kai ɗari-shida. Bayan haka, sun dauki shawara a laƙƙa mata suna "Bal Tapasvi". Sun ƙara shawarce su yi babbar buki mai suna "Shobha yatra" waton bikiʼn murna.

Iƴƴaƴeʼn ƴarinya marigaya suna sanaʼan zinare. Shagoʼn su yana wani wuri mai suna Port Bazaar, a cikin ƙarimin hukumar Secunderabad. Jamaʼa da yawa sun tambaye su dalilin hana yarinya zuwa makarantaʼn boko domin yin azumi.

Ɗaya daga cikin ʼƴan-garin marigaya, mai suna Lata Jain, ta ba da bayani kamar haka;

"Wannan azumi alʼadanmu ne. Shuwagabanin gari suna yaban duk wanda ya cika wannan aikin roƙo, kuma suna bada kyuta. Amma wannan yarinya, ta yi ƙarammi da yawa." Ta ƙara magana da cewa "Wannan yarinya ta kashe kan ta ne, kokuma mu ce an kashe ta ne. Wannan ba azumi ba ne". ʼƳan-uwanta, sun sheida cewa Aradhana ta taɓa azumi na kwana arbaʼin da ɗaya.

ADVERTISEMENT

Kakaʼn yarinya mai suna Manekchand Samdhariya ya faddaɗa cewa; "Ba mu ɓoye komai ba, kowa ya san da cewa Aradhana tana azumi. Wasu ma daga cikin Jamaʼa, sun dauƙi hoto tare da ita. Amma yanzu sun canza baki, suna bamu laifi domin mun bari ta yi azumin kwana sittin da takwas. Mallmai na addinin Jain, su fassara cewa wannan azumi, mai suna "Santhara" na tsofaffi ne, wadanda sun shirya barin duniya.

Wani mutum mai suna Maharasa Ravinder Muniji na garin Kachiguda Sthanak ya bayyana ma ʼƴanjerida na NDTV cewa "ba kaʼida ba ne mu sa mutum azumin dole. Wannan faruwa haɗari ne, kuma ya kamata mu koyi misali daga wannan mumunar abu.

Wata mai himmar aiki-Shanta Sinha- ta ba da umurni na karɓan takadda daga offishin ʼƴan sanda da Hukuma mai Kula da al-hakin  Yara. Ta faɗa cewa bai dace a ƙyale ƙananaʼn yara su yi ganin damaʼn su. Ta ce ya kamata Mallamai na addini su yada haske game da wannan matsala.

ʼƳan-sanda sun fara bincike-bincike game da mutuwaʼr yarinya. Mataimakiʼn babba’n Shugaban ʼYan-sanda ya tabbatar da cewa wannan ya kai ga kunensa da kuma cikin littafai na Hukuma.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT